
Hukumar Zakka da Hubsi ta Jihar Kano ta rabawa mabuƙata 400 buhunhunan shinkafa domin ragewa al’umma, musamman masu ƙaramin ƙarfi raɗaɗin matsin rayuwa da a ke ciki.
Da ya ke jawabi a yayin taron raba kayan abincin, wanda a ka gudanar a harabar hukumar, Darakta Janar l, Alhaji Safyan Ibrahim Gwagwarwa ya ce an rabawa mutanen shinkafar ne duba da halin matsin rayuwa da a ke fama da shi a wannna lokaci.
A cewar sa, rabon kayan zai sauƙaƙawa al’ummar da su ka amfana da tallafin.
Ya ƙara da cewa, Hukumar ta daɗe ta na gudanar da irin wannan aiki, wanda dama ya na dabga cikin aiyukan ta taimakawa masu ƙaramin ƙarfi domin rage musu raɗaɗin talauci.
Babban Daraktan ya ce Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya samar da kuɗin da a ka sayo kayan da a ka raba, inda ya yabawa Gwamnan sabo da irin tallafin da yanke baiwa Hukumar ankan kari ba tare da gajiyawa ba.
A nashi jawabin, Shugaban Hukumar, Usman Yusuf Makwarari ya ce ya zama wajibi su yabawa gwamna Ganduje sabo da irin kulawa da goyon bayan da ya ke baiwa Hukumar, domin ta taimakawa mabuƙata a jihar nan.