
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano a jiya Litinin ya ƙaryata raɗe-raɗin dake yi na cewa ya ƙulla yarjejeniya da fadar shugaban kasa gabanin hukuncin da kotun koli ta yanke ranar 12 ga watan Janairu wanda ya tabbatar da zaben sa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan sa na yada labarai da bayanai, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a Kano a jiya Litinin.
Dawakin-Tofa ya bayyana wata takarda da tuni ta ke yawo tare da nuna wasu yarjejeniyoyi huɗu tsakanin gwamna da fadar shugaban kasa a matsayin wata tatsuniyar da ba ta da tushe balle makama.
Ya bukaci jama’a da su yi watsi da raɗe-raɗin yarjejeniyar a matsayin karya da ke ikirarin gwamnan ya amince da tsallakawa jam’iyyar APC mai mulki da sauran sharuddan yarjejeniya.
“Gov. Yusuf zai na bayyana karara cewa kasancewar ya samu nasarar zabensa ta hanyar kuri’u na al’ummar Kano, da kuma tabbatar da hukuncin kotun koli, ba zai razaba daga duk wani tuggun siyasa ba.
“Bari kuma in tunatar da waɗanda suka maida siyasa sana’a da ke fakewa a karkashin sassaucin shugaban kasa cewa duk wata shawara ko alkiblar siyasa da za a bi a Kano za a tabbatar da shi ne a cikin tsarin doka da ikon zartarwa da ya rataya a wuyan gwamnan zartaswa,” in ji Dawakin-Tofa.