Home Kasuwanci Za mu hukunta duk bankin da ke ɓoye sabbin kuɗi da aka canja wa fasali — CBN

Za mu hukunta duk bankin da ke ɓoye sabbin kuɗi da aka canja wa fasali — CBN

0
Za mu hukunta duk bankin da ke ɓoye sabbin kuɗi da aka canja wa fasali — CBN

A jiya Alhamis din da ta gabata ne babban bankin Najeriya, CBN, ya sha alwashin hukunta duk wani banki da aka samu ya na ɓoye sabbin takardun Naira, inda bankin ya ce ya samar da isassun kuɗin don rarrabawa ga dukkan bankunan kasar.

Kwantarolan bankin na CBN, reshen Kano, Umar Biu ne ya bayyana hakan a yayin taron wayar da kai kan sabon kudin, wanda aka shirya wa ‘yan kasuwa a kasuwar Sabon Gari da ke Kano.

Taron ya samu halartar ’yan kasuwa daga Kasuwar Kwari, kasuwar canji ta Wapa, kasuwar Kofar Wambai, da kuma shahararriyar Kasuwar Kurmi da ke cikin birnin Kano.

Ya ce ‘yan kasuwar suna da ‘yancin kai rahoton duk wani banki da aka samu ko ya na tara sabbin takardun kudi ko kuma ya na cajin kwastomomi kafin su ajiye tsoffin takardunsu na Naira.

“Kuna da ‘yancin kai rahoton duk wani banki da aka samu yana tara sabbin takardun kudi na Naira ko kuma ya ki karban tsoffin takardun ku kafin ranar 31 ga Janairu, 2023.

“Babu wani banki da zai hana karbar tsohon takardun naira har zuwa ranar 31 ga watan Janairu, 2023,” in ji mai kula da reshen.

A cewarsa, babban bankin ya kuma umurci bankunan kasuwanci da su daina biyan kudi a kan kanta a wani bangare na kokarin ganin daƙile nuna fifiko ga kwastomomi.

Ya ci gaba da cewa babu gudu babu ja da baya ga dokar hana karɓar tsohon kuɗi a ranar 31 ga watan Janairun 2023, inda ya kara da cewa duk tsofaffin takardun za su daina aiki a ranar.