
Kamfanin Mai na Ƙasa, NNPC ya yi barazanar hukunta masu defo din mai masu zaman kansu idan su ka ƙi sayar da man fetur a kan farashin gwamnati.
Shugaban Ƙungiyar Dillalan Man fetur ta Ƙasa, IPMAN, Elder Chinedu Okoronkwo shine ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai ta wayar tarho a Kano a jiya Alhamis.
Ya ce kamfanin NNPC ya yi wannan gargaɗi ne a wata ganawa da shugabannin IPMAN a ranar Laraba a Abuja.
A cewar Okoronkwo, NNPC ya yi barazanar dena baiwa masu defo ɗin man fetur idan har su ka ƙi sayar wa a kan farashin gwamnati.
Ya kuma bayyana cewa NNPC ya baiwa shugabannin ɓangaren kula da mai na ƙasa da wajen teku, NMDPRA da su sanya ido a kan tabbatar da umarnin.
Ya ce tun da gwamnatin taraiya ba ta ƙara farashin man fetur ba, to babu hujjar da masu defo masu zaman kan su za su ƙara farashin mai, inda ya jaddada cewa duk wanda ya kauce wa umarnin to zai fuskanci hukunci.