Home Labarai Ibtila’in da ke faruwa a Nijeriya na neman fin karfin mu — Red Cross

Ibtila’in da ke faruwa a Nijeriya na neman fin karfin mu — Red Cross

0
Ibtila’in da ke faruwa a Nijeriya na neman fin karfin mu — Red Cross

Kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya ta ce duk da cewa tana da masu aikin sa kai sama da dubu 800 a duk fadin kasar, ibtila’i da bala’o’i da ke faruwa a kasar na neman fin karfin ta.

Shugaban Red Cross ma kasa, Prince Oluyemisi Adeaga ne ya bayyana haka a Legas yayin taron tara gudunmawa na 2024 da aka gudanar a Legas a ranar Asabar.

Saboda haka Adeaga yayi kira ga masu hannu da shuni da su kara dagewa da bada tallafi wajen ayyukan Red Cross don taimakawa ƴan Najeriya da suka rasa matsugunansu.

Adeaga ya bayyana cewa har yanzu Najeriya ba ta farfado daga bala’in ambaliyar ruwa na 2022 ba sai ga lamarin ya sake afkuwa a 2024, inda ya kara da cewa matsalar jin kai a Maiduguri kadai bayan ambaliyar ruwan da aka yi a baya-bayan nan ta wuce tunani.