Home Kasuwanci IBTILA’I: Gobara ta laƙume ɗaruruwan buhunhunan shinkafa da injinan sarrafa ta a Kano

IBTILA’I: Gobara ta laƙume ɗaruruwan buhunhunan shinkafa da injinan sarrafa ta a Kano

0
IBTILA’I: Gobara ta laƙume ɗaruruwan buhunhunan shinkafa da injinan sarrafa ta a Kano

 

A daren Litinin ɗin da ta gabata ne dai wani ƙaramin kamfanin sarrafa shinkafa da ke kasuwar ƴan shinkafa a Ƙaramar Hukumar Kura ta Jihar Kano ya ƙone ƙurmus sakamakon tashin gobara.

Gobarar ta tashi a kamfanin, mallakar wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Nasiru Suleman, da tsakar daren Litinin, inda ta ƙone buhunhunan shinkafa, masara, dawa da sauransu.

Haka kuma, manyan injinan sarrafa shinkafa guda 8 da ke kamfanin su ma sun ƙone ƙurmus.

Da ya ke zantawa da manema labarai a jiya Talata, Suleman ya ce mutane uku ne su ka kira shi a waya da misalin ƙarfe 1:23 na dare su ka shaida masa cewa kamfanin na sa na ci da wuta.

 

“Ko da na zo wajen, na tarar da jama’a da yawa sun zo don su taimaka, amma wallahi ba wanda ya iya zuwa kusa da rumfar saboda girman wutar ya isa,” in ji shi.

Cikin hawaye da alhini, Suleman ya ce ɗaruruwan buhunhunan shinkafa gyararriya da wacce ba gyararriya ba, gami da masara da dawa, sannan ga injinan gyaran shinkafar guda 8 duk sun ƙone.

“Dole ne na yi kuka sabo da duk illahirin kayan cikin rumfar nan sun ƙone. Manyan injina na gyaran shinkafa gasu nan duk sun ƙone ƙurmus.

Mai kamfanin ya ƙara da cewa dole ya zubar da hawaye sabo da akwai dukiyoyin jama’a da su ka amince masa su ka bashi ya ke juyawa, amma gashi gobara duk ta laƙume su.

 

Ya kuma ce kawo yanzu, ba a san musabbabin gobarar ba, inda ya ƙara da cewa bai san adadin kuɗin da aka yi asarar ba a halin yanzu.

Ya ƙara da cewa”amma babu komai, mun rungumi ƙaddara. Haka Allah Ya tsara. Muma masu kamfanin tafiya zamu yi watarana ba ma kayan kamfani ba.

“Ina godiya ga Allah da ya bar mu da ran mu kuma muna roƙon Sa da ya yafe mana. Allah Ya sakawa duk waɗanda su ka kawo taimako da alheri,”

Rahotanni sun baiyana cewa mutum biyu sun samu ƙuna a jikin su, amma tuni a ka garzaya da su asibiti domin basu kulawa.

A nashi ɓangaren, Babban Sakatare na Hukumar Bada Agajin Gaggawa, Alhaji Sale Jili ya ce sun samu labari kuma suna jajantawa al’ummar kasuwar.

Ya baiyana cewa a yau Laraba za su ziyarci wajen su ga irin asarar da a ka yi kuma za su rubuta rahoto ga Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje domin ganin yadda za a tallafawa wanda abin ya shafa.