
A jiya Talata ne dai mutanen Ƙaramar Hukumar Ɓagwai da ke Jihar Kano su ka sake gamuwa da wani ibtila’i na kifewar kwale-kwale, in da yai sanadiyar rasuwar mutane da dama.
Radio Nigeria ta rawaito cewa a ƙalla mutane 19 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 5 suka tsira da ransu biyo bayan kifewa da kwale-kwalen ya yi da mutane a kan hanyarsu ta zuwa Mauludi.
Gidan rediyon ya baiyana cewa kwale-kwalen mai ɗauke da mutane 43 ya taso ne daga ƙauyen Badau zuwa Ɓagwai ɗauke da ɗaliban wata Makarantar Islamiyya don halartar taron Maulidi a garin Tofa.
Ya zuwa wannan lokacin, masu aikin ceto sun gano gawarwaki 19 da kuma matane 5 waɗanda su ka tsira da ransu.
Tuni a ka garzaya da mutum 5 ɗin da a ka ceto da ransu zuwa asibitin ƙaramar hukumar Ɓagwai domin basu kulawa.
Rahotanni sun ce za’a cigaba da aikin ceto domin nemo sauran mutane 19 a safiyar Laraban nan.
Idan zaa iya tunawa ko a shekaru 13 da suka gabata an taɓa samun irin wannan haɗari a Ɓagwai, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama yayin da wasu kuma su ka tsira, ciki har da sanannen mawaƙin nan ɗan asalin yankin, Aminu Rinji Bagwai.
Ko a ranar 19 ga watan Nuwamba da ya wuce, yara mata guda 7 ne su ka rasu a haɗarin kwale-kwale a hanyar su ta zuwa bikin Maulidi a ƙauyen Gamafoi da ke Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa a Jihar Jigawa.