
Hukumar yaƙi da Cin-hanci mai zaman kanta, ICPC ta maka Shugaban Ƙaramar Hukumar Fagge da ke Jihar Kano, Ibrahim Shehi a gaban babbar kotun jiha.
Daily Nigerian Hausa ta samu bayani cewa ICPC ɗin na tuhumar Shehi ne da laifuka 4 da su ka shafi zargin sama-da-faɗi da kuɗaɗen harajin ƙaramar hukumar.
Lokacin da ICPC ɗin ta kai ƙarar Shehi, sai a ka tura su kotu mai lamba 16 da ke titin Miller a unguwar bamfai cikin birnin Kano.
Jaridar nan ta jiyo cewa a yau Laraba ne dai za a gurfanar da shugaban ƙaramar hukumar da karfe 9 na safe.