
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta kama wata mata mai shafin Twitter mai suna @Simisola, bisa zargin tallata sabbin takardar Naira da aka sauya wa fasali a shafukan sada zumunta.
Mai magana da yawun hukumar, Azuka Ogugua a wata sanarwa a ajiya Laraba, ta ce an kama ta ne sakamakon bayanan sirri da jami’an ICPC su ka samu.
Ta ce wacce ake zargin ta yi amfani da damar da ta samu ta karancin sabbin takardun naira a ƙasa wajen tallata su a yanar gizo.
“An yi imanin cewa ta haɗa kai ne da wasu ɓatagarin ma’aikata a a fannin harkar kuɗi da su ke karkatar da sabbin takardun bayanan da aka fitar daga dakunan banki da hanyoyin biyan kuɗi zuwa “kasuwar bayan-fage,” in ji ta.
Ta kara da cewa matar, wata ‘yar kasuwa ce ta dandalin sada zumunta, da ta yi suna wajen tallan mayukan gyaran fata, sayar da man fetur, harkar tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ta hanyar samar musu biza, da sauran harkokin kasuwanci.
A cewarta, wacce ake zargin a halin yanzu na tsare a hannun ICPC kuma ta na taimakawa hukumar da muhimman bayanai wajen binciken da ta ke gudanarws kan cinikin naira da kuma karancin ta, da kuma matsalar tattalin arzikin da matakin ke haifarwa.
Ta kuma yi bayanin cewa kama wa ce ake zargin ya faru ne sakamakon ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin CBN, ICPC da EFCC wajen aiwatar da sabbin manufofin kuɗi da kuma sake fasalin Naira.