Home Labarai Idan ba karatun PhD za ku yi ba kar ku zo mana jami’o’i da iyalan ku — UK

Idan ba karatun PhD za ku yi ba kar ku zo mana jami’o’i da iyalan ku — UK

0
Idan ba karatun PhD za ku yi ba kar ku zo mana jami’o’i da iyalan ku — UK

Kasar Burtaniya, ta ce daliban kasashen duniya da ke zuwa domin samun digiri na uku ne kadai suka cancanci zuwa yin karatu da iyalansu.

Richard Montgomery, babban kwamishinan Burtaniya a Najeriya ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa a juya Lahadi a Abuja.

Ya ce manufar tsarin ilimi ta sauya a farkon wannan shekarar ga daliban kasashen waje da ke manyan makarantu na kar su zo da iyalan su idan za su yi karatu a Burtaniya shi ne don dakile karuwar daliban kasashen waje da ke kawo iyalansu ƙasashen dake ƙarƙashin UK.

Ya bayyana cewa yawaitar zuwa karatu da iyali yana sanya matsin lamba ga jami’o’i da dama, inda ya ce, dalilin da ya sa aka bullo da wadannan sauye-sauyen kenan.

Montgomery ya kara da cewa, kafin a nada shi a matsayin babban kwamishina a Najeriya, ya yi magana da wasu daga cikin wadannan jami’o’in kan sauya manufofin da aka dade ana yi.

Ya yi nuni da cewa shugabannin jami’o’in sun koka kan dimbin daliban da suka yi nuni da cewa wurin kwana babban kalubale ne, samun damar gudanar da ayyukan kiwon lafiya a karkashin hukumar lafiya ta kasa da kuma samun damar zuwa makaranta idan sauran ɗalibai na zuwa da iyalan su.