
Abdulmajid Dan-Bilki Kwamanda, ƙusa a jam’iyyar APC kuma na jikin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gargaɗi zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da kar ya sake ya janyo Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a farkon makon nan ne dai Tinubu ya gana da Kwankwaso, wanda yai takarar shugabancin kasa a jam’iyyar NNPP, inda rahotanni ke nuni da cewa shugabannin biyu sun yi ganawar ne kan su yi aiki tare a sabuwar gwamnatin da ake shirin kafa wa a ranar 29 ga watan Mayu.
Tuni dai wannan ganawar ta haifar da cecekuce tsakanin magoya bayan APC da na Kwankwaso.
Shima Kwamandan ya bi sahun wadanda ke sukar ƙawancen da ake shirin ƙullawa tsakanin Tinubu da Kwankwaso.
Da ya ke zanta wa da manema labarai a Kano a yau Alhamis, Kwamandan ya ce bai kamata Tinubu ya janyo Kwankwaso ba sabo da Kwankwason bai taimake shi a yayin yaƙin neman zaɓe ba.
A cewar Kwamanda, Kwankwaso bai kai girman da har Tinubu zai kira shi su yi ganawar sirri kan ya taimaka masa a mulkinsa, inda ya ce idan ya yi haka to ya nuna cewa ya fi fita tsohon gwamnan na Kano a kan yan APC da su ka yi masa wahala.
“Wacce irin gudunmawa Kwankwaso zai iya baiwa Tinubu? Kwankwason nan bai taimaka Tinubu ba a lokacin yakin neman zabe sai yanzu da ya ga ya fadi zaɓe kuma zai lallabo ya shigo jam’iyyar mu.
“To gaskiya ina kira ga Tinubu da kada ya sake ya janyo mana Kwankwaso. Ina ba haka ba kuma to wallahi zai hada rigimar siyasa tsakanin arewacin Najeriya da kudancin kasar.
“Idan haka ta tabbata, to za mu yaƙi Tinubu domin dama bai bamu ko sisin sa ba, cancantar sa mu ka gani mu ka yi masa kamfen.
“Sabo da haka mu ba za mu yarda da wannan ba. Idan har Tinubu ya janyo Kwankwaso zuwa APC to sai mun yaƙi Tinubun domin ƴan arewan da ya sani ba irin na da ba ne. Na yanzu wayayyu ne,” in ji Kwamanda.