
Nyesom Wike, Gwamnan Jihar Rivers, ya ce idan a ka zaɓe shi a matsayin shugaban kasa, ‘yan fashin jeji za su tsere da zarar sun ji an kira sunansa.
Da ya ke magana a wani taro da wakilan jam’iyyar PDP daga jihar Taraba a ranar Alhamis, Wike ya ce shi zai tinkari ƴan fashin dajin da yakin.
Tuni dai Gwamnan ya nuna sha’awarsa ta tsaya wa takara a jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Wike ya ce zai farantawa ƴan Nijeriya rai saboda yana da karfin magance matsalolin kasar.
“Matsala daya da ya kamata gwamnatinmu ta PDP ta magance ita ce ta magance matsalar rashin tsaro a ƙasar nan. Idan ba haka ba babu yadda za a yi tattalin arziki ya bunkasa,” inji shi.
“Idan ƴan bindiga su ka ji sunana za su gudu domin zan tinkare su ne da yaƙi. Zan zama babban kwamanda a yaƙin da zan yi da su a aikace.
“Zan riƙa jan ragamar ayyuka, samar da tsaro, noma da tattalin arziki tare da sojoji. Zan ba da umarnin kowane ɓangare na rayuwa wanda zai faranta wa ƴan Najeriya farin ciki. Hakan ya faru ne saboda ina da karfin magance matsalolin Nijeriya.”