
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi ya ce ba zai yi bita-da-ƙulli ko gallaza wa gwamnatin Muhammadu Buhari da sauran gwamnatocin baya da su ka shuɗe ba idan aka zabe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2023.
Da ya ke yiwa manema labarai jawabi a jiya Juma’a bayan kaddamar da Datti Baba-Ahmed, a matsayin mataimakin takararsa a zaben, Obi ya ce shi burinsa shine ya toshe kafofin zirarewar kuɗi da kuma ciyar da ƙasar gaba.
“Game da binciken gwamnatin da ta shuɗe, bari in gaya muku: kun ga ina jayayya da cewa ba za ka iya rufe shagon ka sannan ka bu ɓarawaon da yai maka sata ba ba, wadanda ke duban jiya da yau kawai, to tabbas za su rasa gobe. Allah bai ba mu idanu a baya ba, Ni nawa shine in rika kallon gaba,” in ji Obi.
“Idan ka shigo gwamnati a yau, ka dakatar da zirarewar kuɗaɗe, to kuwa za ka samu haɓɓakar . Ba zan kasance cikin kowane nau’i na cin zarafi ko bita-da-ƙulli ba, ba zai faru ba. Dole dai ƴan Najeriya su yi rayuwa cikin doka da oda.
“Amma zan iya gaya muku nan take. Idan kai kana shugaba, ko shugaban karamar hukuma ko gwamna ko shugaban kasa ba ka sata ba, danginka ba sa sata, kuma wadanda ke kusa da kai ba sa sata, za ka rage kashi 70 cikin 100.”