
Sarki Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa kowane musulmi imaninsa yana cika ne idan ya rungumi kowace irin ƙaddara da ta same shi
“Saboda haka ya zama wajibi mutum ya kasance mai godiya ga Allah kan kowacce ƙaddara mai kyau ko saɓanin haka.
“Dole ne mu yi imani cewa duk abin da muka samu ƙaddarawar Allah ce kuma duk abin da ya suɓuce mana daga wurinSa ne.
“A yanzu muna dosar watan Zhul Hijja wanda saboda falalarsa yana da muhimmanci mu dage da addu’o’i a cikin waɗannan kwanaki.”
Huɗubar Sarki Sanusi II na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da dambarwa kan kujerar sarautar Kano tsakaninsa da Sarki Aminu Ado Bayero wanda Gwamnatin Kano ta tuɓewa rawani.
Rfi (Radio France)