
Hukumar Ba da Lamuni ta Duniya, IMF, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta cire tallafin man fetur da na wutar lantarki gaba ɗaya a farkon shekarar baɗi.
IMF ta yi kiran ne a wani kundin sakamakon bincike da ta yi a ƙarshen ziyarar da ma’aikatanta su kawo Nijeriya, a ƙarƙashin jagorancin l Artile IV.
Hukumar ta kuma i kira da Nijeriya ta yi garambawul hidimomin kuɗaɗe, canjin kuɗaɗe, kasuwanci da tsarin mulki domin gyara matsalolin da su ke hana ƙasar ci gaba.
A sanarwar da ta fitar, IMF ta ce ya kamata a cire tallafin man fetur da na wutar lantarki domin hakan ne zai zama wani ginshiƙi na gyaran tattalin arzikin ƙasar nan.