Home Labarai ‘ina bala’in son matata’, in ji ɗan kasuwar da ya musanta sakin matarsa a Kaduna

‘ina bala’in son matata’, in ji ɗan kasuwar da ya musanta sakin matarsa a Kaduna

0
‘ina bala’in son matata’, in ji ɗan kasuwar da ya musanta sakin matarsa a Kaduna

Wani ɗan kasuwa, Hassan Abubakar, a jiya Talata ya musanta cewa ya saki matarsa, Bashirat Abdulrazak a wata kotun Shari’a da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna.

Abubakar ya shaida wa kotun cewa yana son matarsa ​​kuma ba shi da niyyar sakin ta.

“Muna da ɗa tare da ita. Na dawo gida daga kasuwa wata rana, sai na ga cewa ta kwashe duk kayanta daga gidan.

“Alhali ba mu samu wata matsala ko rigima ba”, in ji shi.

Tun da fari dai mai shigar da karar ta shaida wa kotun cewa mijin nata ya yi mata furuci guda daya na saki.

Ta roki kotu da ta tabbatar da sakin.

“Ina kuma son ya ɗauki nauyin ɗan sa kuma ya biya adadin kudin da zai iya biya na ciyarwa duk wata,” in ji ta.

Alkalin kotun, Rilwanu Kyaudai, ya bukaci mai karar da ta gabatar da shaidu domin tabbatar da zargin da ta ke yi.

Ya ɗage sauraron karar har zuwa ranar 19 ga watan Janairu domin ma’auratan su binciko hanyoyin sasantawa, sannan kuma mai karar ta gabatar da shaidunta idan sulhun ya gaza.