
Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress, AAC, Omoyele Sowore, ya bayyana fatansa na ganin al’ummar Kano za su zabi jam’iyyarsa a zaben 2023..
Sowore ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yammacin ranar Juma’a, jim kaɗan bayan kaddamar da yakin neman zabensa na shugaban kasa, inda ya ce ya kaddamar ne a Kano saboda Kano ‘Majalisar Jama’a ce.
“Muna da kwarin gwiwa cewa tare da goyon bayan jama’a da hadin gwiwa, AAC za ta gina wa al’ummar Nijeriya, kasar da za su yi alfahari da ita.
“Za mu kewaye fadin kasarmu don karfafa wa da hada kan jama’armu don kawar da gurbatattun ƴan siyasa da kuma ceto kasar .”
Har ila yau, Sowore ya caccaki sake fasalin kudin Naira da gwamnati mai ci ta yi, yana mai cewa hakan zai kara tabarbare tattalin arzikin kasa.
“Tattalin arzikin ya tabarbare, ga matsalar rashin aikin yi, karancin albashi, hauhawar farashin kayayyaki, ga kuma tallafin gwamnati ya yi ƙaranci, inda hakan ke ƙara tura mutane cikin ƙangin talauci,” in ji shi.
Daga nan sai ya tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa jam’iyyarsa za ta gyara ilimi tare da kara zuba jari a muhimman ababen more rayuwa musamman makamashi.