Home Labarai Ina jin zafin yajin aikin ASUU a zuciya ta, in ji Buhari

Ina jin zafin yajin aikin ASUU a zuciya ta, in ji Buhari

0
Ina jin zafin yajin aikin ASUU a zuciya ta, in ji Buhari

 

 

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake yin kira ga kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da ke yajin aikin da su koma ajujuwa tare da ba su tabbacin shawo kan matsalolin da suke fuskanta ta hanyar karancin kayan aiki.

Shugaban, wanda ya sake nanata kiran a wani jawabin da ya yi wa ƴan ƙasa ta kafafen yaɗa labarai a yau Asabar a Abuja, ya ce ya na matukar takaicin yadda ilimin jami’a ke ci gaba da tabarbarewa a kasar nan.

Jawabin na kai-tsaye wani bangare ne na bikin bikin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai na kasar.

A cewarsa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da samar da kudade a gida da kasashen waje don samar da tallafin ilimi domin tabbatar da cewa ‘yan kasa sun samu ilimi da kwarewa a sana’o’i daban-daban.

“Dole ne in furta cewa ina jin zafi sosai game da taɓarɓarewar karatun jami’a a kasar nan.

“Ina amfani da wannan bukin ranar samun ‘yancin kai ne domin nanata kirana ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ke yajin aiki da su dawo ajujuwa tare da ba su tabbacin shawo kan matsalolin da suke fuskanta duk da karancin kudade da mu ke fuskanta.

“Wannan gwamnatin ta samu ci gaba mai inganci wajen gyara wadannan al’amura da aka kwashe sama da shekaru goma sha daya ana yi,” in ji shi.