
Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Aliko Ɗangote ya baiyana yadda ƙaninsa, Sani Ɗangote ya rasu a gabansa.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Sani Ɗangote, wanda shine Mataimakin Rukunin Kamfanoni Ɗangote, ya rasu a wani asibiti da ke Miami a Amurka.
Yayin da ya tarbi Jagoran Jam’iya mai Mulki, APC, Bola Tinubu a gidansa da ke Kano a ranar juma’a, Ɗangote ya baiyana cewa a gabansa da maihaifiyarsu, da ƴaƴan Sani Allah Yai masa cikawa.
Ɗangote ya ƙara da cewa, da su ka je asibitin, a lokacin da a ke duba marigayin, likitocin sun faɗa musu cewa nan da awa ɗaya zai rasu.
Ya ƙara da cewa lokacin da marigayin ya ke kwance an jona masa na’ura, “abin baƙin ciki da ciwo shine cewa mu na kallo ta na’ura har ya rasu. Wannan abu da tashin hankali ya ke.
“Amma haka Allah Ya tsara. Kuma kowa zai rasu. Ba wanda ya san wanene gawar fari. Ko mai kuɗi ko talaka. A matsayin mu na musulmai, mun yi imani da mutuwa.
“Mu na riƙon Allah da Ya jiƙansa da gafara.
“Mai girma Gwamna, mu na godiya da wannan karamci da ka ke mana. Mun gode sosai, Allah Ya saka da alheri,”
A nashi jawabin, Tinubu ya baiyana cewa kuɗi ba zai iya siya rayuwa ba, inda ya ce idan mutuwa ta zo ba abinda a ka isa a yi.
Ya yi kira ga Dangote da sauran dangin marigayin da su dage da yi masa addu’a, in da ya ce ya zo Kano me domin yin ta’aziyar mamacin.