Home Labarai Ina maka fatan alheri, Tinubu ya faɗa wa Ngelale yayin da ya amince da ajiye aikinsa

Ina maka fatan alheri, Tinubu ya faɗa wa Ngelale yayin da ya amince da ajiye aikinsa

0
Ina maka fatan alheri, Tinubu ya faɗa wa Ngelale yayin da ya amince da ajiye aikinsa

Shugaba Bola Tinubu ya amince da ajiye aiki da Cif Ajuri Ngelale ya yi a matsayin mai magana da yawunsa.

A safiyar jiya Asabar, Ajuri ya ba da sanarwar cewa zai tafi hutu na dindindin don tunkarar yanayin rashin lafiya da ya ce “a halin yanzu yana shafar iyalin sa”.

Ya ce ya mika takarda ga ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a daren jiya Asabar, fadar shugaban kasar ta ce Tinubu ya karbi takardar kuma ya gode wa Ngelale kan hidimar da ya yi wa kasa.

“Shugaban ya karbi takardar daga Cif Ajuri Ngelale, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a da kuma mai magana da yawun shugaban kasa da kuma wakilin shugaban kasa na musamman kan harkokin sauyin yanayi, inda ya sanar da matakin da ya dauka na tafiya hutu bisa wasu dalilai na rashin lafiya

“Shugaban kasa ya amince da dalilansa na hutun, ya fahimce su sosai kuma yana tausayawa al’amuran da suka kai ga yanke wannan hukunci mai wuya.

“Yayin da yake mika addu’o’insa da fatan alheri ga Cif Ngelale da iyalansa a wannan lokaci mai cike da kalubale, Shugaban na fatan samun sauki cikin gaggawa da kuma cikakkiyar lafiya,” in ji sanarwar.