Home Siyasa Ina nan daram a APC, in ji A A Zaura

Ina nan daram a APC, in ji A A Zaura

0
Ina nan daram a APC, in ji A A Zaura

 

Ɗaya da ga cikin ƴan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC, Abdulkarim Abdulsalam, wanda a ka fi sani da A A Zaura ya musanta labarin ficewarsa daga Jam’iyyar APC zuwa NNPP.

A A Zaura ya bayyana hakan ne a sahihin shafinsa na Facebook a jiya Lahadi da daddare.

Tun bayan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya baiyana mataimakinsa, Nasiru Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamna a jam’iyar, a ka fara sakin hoton A A Zaura da Kwankwaso, inda ake raɗe-raɗin cewa zai sauya sheƙa zuwa NNPP.

Sai dai kuma nan da nan Zaura ya maida martani, inda ya ce “da yammacin nan, an jawo hankali na kan wasu wallafe-wallafe a kafafen sada zumunta na zamani, cewa “wai” na koma jam’iyar NNPP. Wannan labari ƙarya ne.

“A wannan lokaci babu dalilin canza jam’iya domin mun shigo APC ne don mu gina wannan jiha tamu.

“Hoton da ake amfani dashi don nuna cewa “wai” na koma waccan Jam’iya, hotone wanda aka ɗauka a watannin baya lokacin da naje ta’aziyyar rasuwar mahaifin His Excellency, Rabiu Musa Kwankwaso – ALLAH Ya ƙara Rahama ga Baba” inji A A Zaura.

A A Zaura da Kwankwaso
A A Zaura ya yi kira ga Al’umma da suyi birins da irin wadannan labarai da basuda tushe balantana Makama.

Ana dai zargin Zauran ya dau Matakin sauya shekar ne Saboda yadda aka rawaito Cewa Gwamna Ganduje ya nuna goyan bayansa ga Mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo a Matsayin Yan takarar gwamna da Mataimaki.