
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya suffan ta kan sa a matsayin mutum mai basira da gogewa da zai iya ceto Nijeriya da ga matsalolin da ta ke ciki idan a ka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.
Saraki, ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar adawa ta PDP ya baiyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai garin Akure domin neman goyon baya da ga wakilan da za su zaɓi ƴan takara a zaɓen fidda gwani mai zuwa.
Ya ce zaɓen 2023 wani canji ne gagarumi a ƙasar nan, inda ya ƙara da cewa ƙasar na bukatar shugaba da ya fahimci tattalin arziki ya kuma sadaukar da kansa wajen ceto Najeriya daga mawuyacin halin da ta tsinci kanta.
A cewar Saraki, gogewar sa a siyasa ce ta sanya ya zama cewa yana da ƙwarewar da zai iya riƙe ƙasar nan.
A nashi jawabin, Fatai Adams, Shugaban Jam’iyar PDP na jihar ya ce Saraki ya gyara majalisar dokoki ta ƙasa lokacin yana shugaban majalisar dattawa.
Adams ya ce a lokacin yana shugaban majalisar, ya sanya ƙasar nan ta zama abar alfahari kuma ya dage wajen gudun zama ɗan amshin shata a wajen shugaban ƙasa.