
Gwamnatin Taraiya ta Indiya ta sahale da ƙudurin ƙara shekaru mafi ƙarancin shekarun auren fari ga mace da ga 18 zuwa 21, kamar yadda rahotanni su ka rawaito da ga kafafen yaɗa labarai na ƙasar a yau Alhamis.
Rahotanni da ga ƙasar sun baiyana cewa an yanke hukunci kan ƙudurin ne a taron majalisar zartaswa ta ƙasar a jiya Laraba.
A halin yanzu, mafi ƙarancin shekarun auren fari ga maza shekaru 21 , ga mata kuma shekaru 18, inda yanzu a ka sahale ƙudurin cewa mafi ƙarancin shekarun auren fari ga mata ya yi daidai da na maza.
“Bayan sahalewar ƙudurin da majalisar zartaswa ta yi, gwamnati za ta yi garambawul ga dokar hana auren yara ta 2006, inda da ga bisani a yi kwaskwarima ga dokar aure ta musamman ta 1954 da kuma sauran dokoki kamar su dokar aure ta Hindu ta 1955,”
Majalisar zartaswar ta sahale da ƙudurin ne wanda Cibiyar Kawo Sauye-sauye ta India, NITI ta miƙa.