
7
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ce ta ƙaro na’urar yin katin zaɓe guda 209 zuwa Jihohin Kudu maso Gabas guda biyar, Legas kuma Kano domin rage cunkoso a cibiyoyin yin katin zaɓe wato CVR a ƙasar nan.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da kwamishinanta kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe ya fitar a Abuja a jiya Juma’a.
Okoye ya ce hukumar ta samu rahotanni daga jihohi da ke nuni da ƙaruwar jama’a ɗumbin da ke son yin yin rijistar zabe da kuma kalubalen da jihohin suke fuskanta a fadin ƙasar nan.
Okoye ya ce rahotannin sun nuna cewa a wasu jihohin, ba zato ba tsammani a ka samu ƙaruwar ɗumbin al’umma masu a yi musu katin zaɓe.
“Saboda haka, Hukumar ta kira wani taro na gaggawa tare da daukacin kwamishinonin zabe (RECs) a ranar Alhamis, don duba halin da ake ciki, ta yadda ‘yan Najeriya da suka cancanta da ke son yin rajista su samu damar yin hakan.
“Wajibi na gaggauta tura karin na’urorin yin katin zaɓe domin rage cunkoso a cibiyoyin rajistar a matsayin fifiko.
Okoye ya ce ƙarin kwatsam da a ka samu na masu yin katin zaɓe wani tabbaci ne na karin kwarin gwiwa da ‘yan Najeriya ke da shi kan harkokin zabe na INEC.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da tabbatar da cewa amincewar da ƙwarin gwiwa a yan ƙasa ke da shi a kan INEC ya ɗore.