Home Siyasa Tinubu ya lashe zaɓen 2023

Tinubu ya lashe zaɓen 2023

0
Tinubu ya lashe zaɓen 2023

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Sanata Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Tinubu, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Legas ne, ya samu jimillar kuri’u miliyan 8,794,726 inda ya doke manyan abokan hamayyarsa; Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u miliyan 6,984,520 da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu kuri’u miliyan 6,101,533 daga cikin kuri’u miliyan 24,965,218 da aka kada.

Shima Sanata Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya zo na hudu da kuri’u miliyan 1,496,687.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce an sanar da dawowar Tinubu kuma an zabe shi bayan ya cika sharuddan zaɓe.