
Hukumar zaɓe Mai zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta ce tana kyautata zaton a ƙalla ƴan Nijeriya miliyan 90 za su kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen kasa mai zuwa na 2023.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara ofishin hafsan sojin saman Najeriya IO Amao a Abuja babban birnin kasar.
Shugaban hukumar zaben ya nemi taimakon rundunar sojan saman Najeriya wajen ganin an isar da kayan zaɓe a ƙananan hukumomi a lokaci guda lokacin zabe.
Yakubu yace aiki da rundunar shine mafita wajen kare yiwuwar samun tsaiko wajen isar da kayayyakin zabe musamman a yayin da hukumar ke kokarin ganin tayi zaben gwamna a jihar Ekiti akalla nan da makwanni biyu masu zuwa.
Ya jaddada muhimmancin kai kayayyakin zabe a runfunan zabe 190,000 lokacin zaben ‘yan majalisu a duk fadin kasar, wanda ake bukatar ganin anyi zabe a lokaci guda wato daga karfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na yamma.
Yayin jawabinsa hafsan sojin saman Nijeriya, Amao yace rundunar a shirye take don ganin ta taimakawa hukumar ta INEC wajen gudanar da ayyukan zabe ba tare da wata matsala ba.