Home Siyasa INEC za ta hukunta ma’aikata 23 bisa yin rijistar masu zaɓe ba bisa ƙa’ida ba

INEC za ta hukunta ma’aikata 23 bisa yin rijistar masu zaɓe ba bisa ƙa’ida ba

0
INEC za ta hukunta ma’aikata 23 bisa yin rijistar masu zaɓe ba bisa ƙa’ida ba
Sakamakon yin rijistar masu zaɓe sama da guda ɗaya da doka ta tanada a aikin yin rijistar da a ka kammala a kwanan nan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta fara ɗaukar matakin hukunta ma’aikatanta 23.
Bayanai daga hukumar sun nuna cewa wasu daga cikin ma’aikatan, su 23 sun yi yunkurin yi wa wasu masu zaɓe na jabu rajista har sau 40, kamar yadda shugaban INEC ta ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana a jiya Laraba a yayin taro da jam’iyyu na zangon shekara na 3 a Abuja.
Yakubu ya ce hukumar ta gano ma’aikatan na ta 23 kuma za ta yi musu hukunci mai tsanani bayan da su ka yi yunkurin yin rajista da dama hawa ga masu zaɓe.
Shugaban ya kuma bayyana hakan ne a daidai lokacin da majalisar ba da shawara, IPAC ta kada kuri’ar amincewa da shi kan sabbin dabarun da ya ɓullo da su na sake fasalin tsarin zabe.
Gabanin babban zaben na shekara mai zuwa, INEC ta kuma bayyana cewa akalla ƴan Nijeriya miliyan 93.5 ne su ka cancanci shiga zaben a matsayin masu kada kuri’a, tare da nuna cewa ƴan ƙasa miliyan 12.29 ne suka samu nasarar kammala rajistar kada kuri’a.