
Hukumar zabe ta Najeriya (INEC) ta ce ba ta karbi sunayen Shugaban Majalisar Dattawan kasar Ahmed Lawan da tsohon Ministan Harkokin Niger Delta Godswill Akpabio a matsayin ‘yan takarar majalisar dattawa ba.
Hukumar ta ce ta ki karbar sunayen mutanen biyu a matsayin dan takara na shiyyar Yobe ta Arewa da kuma na shiyyar Arewa maso Yamma ta Akwa Ibom sakamakon takaddamar da ke tattare da zaben fitar da gwanin da aka ce an zabe su a jam’yyar APC mai mulkin kasar.
Da take mayar da martani kan wani rahoto da aka sa a intanet wanda a ciki aka zargi hukumar da cewa ta sauya takardun sunayen ‘yan takarar da aka gabatar mata wadanda suka yi nasara domin shigar da sunayen Lawan da Akpabio, INEC ta ce sam-sam ba ta karbi sunan kowanne daga cikinsu ba.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da kwamitin ilmantar da masu kada kuri’a na hukumar Festus Okoye, ya fitar, hukumar ta ce: “Domin fayyacewa takarda EC9 ( ta mika sunayen ‘yan takara da jam’iyyu suka yi) ita ce takardar da jam’iyyu suka sanya a shafin hukumar zaben na karbar sunayen ‘yan takarar da suka zaba. An nuna wannan karara a saman takardar wadda aka karba ranar 17 ga watan Yuni na 2022 a lokacin da aka rufe shafin.
“Abin da ya biyo baya shi ne wallafa bayanan takardun ‘yan takarar da aka zaba, wanda aka yi bayan mako daya. Hukumar ba ta wallafa bayanan takardun mutanen biyu ba da ake magana.
Sanarwar ta kara da cewa : “Matakin hukumar ya janyo matakin shari’a wadda har yanzu ake yi. Saboda haka abu ne da ya saba hankali a je a mika wata takarda ta daban da aka yi sauye-sauye da ake cewa an yarda da mutanen biyu a matsayin ‘yan takara yayin da maganar ke gaban shari’ar.”