
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta sanar da dakatar da zaɓen cike-gurbia wasu mazabu, sakamakon tarzoma, rashin bin ka’ida da kuma sace ma’aikatan zabe.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da:
Kunchi/Tsanyawa State Constituency a jihar Kano, isa daukacin rumfunan zabe guda goma da ke karamar hukumar Kunchi saboda fasa akwatin zabe, tarzoma da dabanci.
A mazabar Ikono/Ini da ke Akwa Ibom kuma, dakatar da zaben ya shafi rumfunan zabe guda biyu (Village Hall, EdemUrua 003 in Ini LGA da Village Hall Mbiabong Ikot Udo 003 in Ikono LGA) inda ‘yan daba suka kwashe duk kayan zaben.
Sai kuma dakatar da zabuka a dukkan rumfunan zabe guda takwas inda ba a samu ainihin takardar sakamakon zaben da masu jefa kuri’a za su yi amfani da ita ba kafin a fara zaben.
Matakin dakatarwar da INEC ta yanke ya yi daidai da tanadin sashe na 24 (3) na dokar zabe, 2022.
Hukumar ta ce za a sanar da karin matakan da suka dace ga mazabun da abin ya shafa bayan taron hukumar a ranar Litinin.
INEC ta yi kira ga jami’an tsaro da su binciki lamarin, yayin da hukumar ta yi alkawarin yin cikakken bincike kan duk wani sabani da ya shafi jami’anta.