Home Labarai INEC ta ajiye 28 ga Afrilu domin fara shirin yiwa Melaye kiranye

INEC ta ajiye 28 ga Afrilu domin fara shirin yiwa Melaye kiranye

0
INEC ta ajiye 28 ga Afrilu domin fara shirin yiwa Melaye kiranye

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta reshen jihar Kogi, ta bayyana cewar, ta ajiye ranar 28 ga watan Afrilu domin fara shirye shiryen yiwa Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma Dino Melaye kiranye, inda Sanatan yake cewa babu wani abu da yake tsoro kan hakan.

Kwamishinan zaben jihar, James Apam, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, yace, batun fara shirin yiwa Sanatan kiraye zai fara ne a ranar Asabar ta karshen watan Afrilu mai zuwa.

Haka kuma, a lokacin da yake mayar  da martani akan wannan ikirari na hukumar zabe, Sanata Melaye yace babu wani abu da zai tsora ta shi game da batun yi masa kiranyen.

Melaye ya bayyana a shafinsa na Twitter inda yake nuna kwarin guiwa da cewar shi ne da nasara a duk abinda za’a shirya masa.

Wannan yana zuwa ne kwana guda bayan da Sanata Melaye yayi wani faifan bidiyo yana kalubalantar Gwamnan jihar.

Mista Melaye ya rubuta “Babu wani abu da zai bani tsoro. Wannan abin tur ne da ba shi da wani tasiri. Tuni na riga na kai kukana ga kotun koli ta najeriya, dan haka INEC ba su da wani abu da zasu iya. Ina da cikakkiyar gamsuwa da mutanan mazabata ba zasu kware mun baya ba”

“Mutanan mazabata babu wani wanda ya sanya hannu domin dawo da ni gida, Gwamna yahya Bello ne kawai yake kidansa kuma yake rawarsa”

“Waye ma zai iya gane sa hannun da yayi kama da na mutanan Taiwan. Bata lokaci ne biyewa irin wannan batu. Gaskiya dai sunanta gaskiya.