
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta umarci lauyanta da ya kare rahoton da kwamitin sa-ido kan zaɓen fidda-gwani na ƴan majalisar dattawan APC na Yobe ta Arewa ya gabatar, wanda ya tabbatar da Bashir Machina a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta INEC, Festus Okoye ya fitar, hukumar ta ce daga yanzu za ta sake duba matakan da lauyoyin ta suka shigar a kotun domin samun daidaito da matsayar ta.
“An jawo hankalin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a kan wani korafi na martani da aka ce an shigar a babbar kotun tarayya da ke Damaturu, bangaren shari’a dangane da zaɓen fidda-gwani na ‘yan majalisar dattawan Yobe ta Arewa.
“Duk da cewa batun na gaban kotu, kuma ba tare da kin bin umarnin kotu ba, hukumar ta sake nanata matsayin ta a baya na cewa ta tsaya kan rahoton kwamitinta na sa ido kuma a kan wannan rahoton ne hukumar ta ƙi buga suna da takardun ƴan takarar Sanatan Yobe ta Arewa.
“Hukumar ta kuma umurci lauyoyin waje da aka yi wa bayanin su gudanar da wannan al’amari don samun daidaito, , wanda ya yi daidai da rahoton da kungiyarmu ta sanya ido,” in ji Okoye.
A tuna cewa a kokarin samun kyakkyawan hukunci ga shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, lauyan INEC, Onyechi Ikpeazu, SAN, ya saɓa wa matsayin hukumar ta hanyar bata sunan zaɓen fidda gwani na ranar 28 ga watan Mayu.
DAILY NIGERIAN ta ruwaito yadda Ikpeazu, a cikin takardar shaidar ya ce jami’an jam’iyyar APC na jihar Yobe ne suka gudanar da zaben fidda-gwani ba kwamitin jam’iyyar na kasa ba kamar yadda doka ta tanada.
Sai dai wannan matsayi ya ci karo da takardar shaidar da hukumar INEC ta fitar da lauyan Machina, Ibrahim Bawa, SAN.