Home Labarai Injin jirgin Faransa ya tarwatse a sararin samaniya

Injin jirgin Faransa ya tarwatse a sararin samaniya

0
Injin jirgin Faransa ya tarwatse a sararin samaniya

A ranar Asabar ɗin nan ne injin jirgin Air France kirar A380 na ƙasar Faransa ya yi fata-fata a sararin samaniya a daidai tekun Atlantic.

Hankalin fasinjojin ya yi matuƙar tashi yayinda su ka ji wata ƙara kuma jirgin ya fara karkarwa.

Yanda injin ya tarwatse

Sai dai matuƙin jirgin ya yi nasarar jan akalarsa har zuwa wani filin sauƙar manyan jirage da ke kusa a yankin Goose Bay na garin Newfoundland da ke ƙasar Canada.

Al’amarin ya faru ne lokacin da jirgin, wanda ya tashi daga birnin Paris zuwa birnin Los Angeles da ke Amurka, ya kai ƙolokuwar nisan kafa dubu talatin da takwas (38,000ft).

Jirgin wanda ke da injina huɗu ya sauƙa lafiya a wannan filin sauƙar jiragen, kuma babu abin da ya samu fasinjojin.