
Al’ummar Igbo, da a ka fi sani da Inyamirai, mazauna jihar Kano sun amince da zaɓen dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Eze Ndigbo na Kano, Ikechukwu Akpudo ne ya bada wannan tabbaci a madadin al’ummar sa lokacin da Ibrahim Ali-Amin (Little), babban mai yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a Kano ya kai masa ziyara a fadarsa.
Eze ya bayyana Abubakar a matsayin wanda ya yi aiki wajen hadin kan kasa.
“Zabin ‘yan Nijeriya shi ne Atiku, domin shi kadai ne zai iya kayar da Tinubu.
” Ya na takara a karkashin babbar tuta. Wani dalili kuma shi ne, ba za mu iya tallafawa tikitin musulmi da musulmi ba. Muna son samun daidaiton tikitin don tabbatar da adalci,” inji shi.
“Kamar yadda kuke gani, kwanaki ne da za a gudanar da zaɓe amma babu wani a cikinmu da zai ƙaura zuwa mahaifarsa don yin zabe. A nan ne muke yin zabe tare da danginmu. Muna zaune a nan, kuma kasuwancinmu suna nan.
“Addu’ar mu ita ce a yi zabe lafiya. Mun yanke shawarar cewa kalubalen da kasar nan ke fuskanta a yanzu Atiku Abubakar ne kadai zai iya magance matsalar.
A nasa bangaren, Mista Ali-Amin ya bayyana cewa, ‘yan kabilar Igbo mutane ne masu son zaman lafiya da su ka yi shura a harkokin kasuwanci.
Ya yi kira gare su da su yi amfani da kuri’unsu yadda ya kamata domin su samu ribar dimokuradiyya tare da jama’arsu.
Ya ƙara da cewa Atiku Abubakar zai tafi da kowacce al’umma a kasar nan ba tare da bambanci ba
kabila, kasar nan ta yi masa yawa, saboda haka, yana so ya mayar wa kasarsa ta hanyar samar da ingantaccen shugabanci mai nagarta ga ‘yan Najeriya.