
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta IPMAN, ta yi kira ga tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i da su daina yin kalaman da basu dace ba a kan harkar mai da iskar gas.
Kungiyar ta ce, da halin da kasar ke ciki a na tattalin arziki, cire tallafin man fetur baki ɗaya zai kara jawo wa ƴan Najeriya wahala, musamman talakawa.
Kungiyar ta IPMAN ta mayar da martani ne kan kalaman Sanusi a wajen taron tattalin arziki da zuba jari na Kaduna karo na 7, inda ya ji tausayin shugaban kasa mai jiran gado saboda irin kalubalen tattalin arzikin da ke jiran sa, musamman batun tallafin man fetur da kuma biyan basussuka.
Shugaban kungiyar IPMAN, reshen Arewa, Alhaji Bashir Danmalam ne ya bayyana hakan yayin da yake zanta wa da manema labarai a Kano a yau Talata.
A cewar Danmalam, tsohon gwamnan babban bankin kasa da El-Rufa’i sun dade suna magana kan cire tallafin a duk fage da suka samu kansu.
“Abin da zai faru bayan an janye tallafin iskar gas (desiel), farashin duk wani abu da za ka yi tunani ya tashi a matsayin litar dizal a yanzu ana sayar da shi a kan N850,” in ji Shugaban IPMAN.
“Tuni aka fara yin gyare-gyare a fannin mai ta hanyar zartar da dokar PIA da shugabannin kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu.
“Dole ne a yaba wa mahukuntan kamfanin na NNPC kan yadda suka tsaya tsayin daka wajen ganin an zartar da dokar masana’antar man fetur (PIA) tare da aiwatar da ita ga wasikar.
Game da maganar da Sarki Sanusi ya yi a kan yawan man fetur da ake amfani da shi a kasa, Danmallam ya hore shi da ya zo su kai shi defo-defo domin ya tabbatar da cewa akwai isasshen man fetur kuma ya fahimci cewa shigo wa da shi a ke yi ko ba shigo wa da shi ƙasar nan a ke ba.
Ya ƙara da cewa akwai lokacin a IPMAN ta rubuta wa Shugaba Buhari da ya kafa kwamiti, a haɗa da hukumar kididdiga ta ƙasa, NBS domin binciken yawan man fetur da ake amfani da shi a kasa.
“Sabo da haka ina kira ga shugabannin nan biyu da su maida hankali kan abubuwan da za su amfani talakawa, maimakon yin maganganu a kan kudurorin da ba na talaka ba ne,” in ji shi