Home Kasuwanci IPMAN ta janye umarnin rufe gidajen mai da ta baiwa mambobinta

IPMAN ta janye umarnin rufe gidajen mai da ta baiwa mambobinta

0
IPMAN ta janye umarnin rufe gidajen mai da ta baiwa mambobinta

Kungiyar Dillalan Man man fetur Mai zaman Kanta ta Ƙasa, IPMAN, ta janye umarnin dakatar da ayyuka da ta baiwa mambobinta a fadin kasar.

Tun daafarko kungiyar ta IPMAN, a yau Talata ta bukaci mambobinta a fadin kasar da su rufe gidajen mai har sai baba-ta-gani.

Shugaban kungiyar ta IPMAN a jihar Borno, Mohammed Kuluwu ne ya bada umarnin.

Sai dai kuma a wani martani na gaggawa, shugaban IPMAN na kasa, Chinedu Okoronkwo, ta hannun shugaban kungiyar shiyyar Kano, Bashir Dan-Malam a yau Talata ya janye umarnin.

Ya ce umarnin ya biyo bayan taron da aka yi tsakanin mahukuntan hukumar kamfanin NNPC da kuma na IPMAN da masu ruwa da tsaki, inda hukumar ta NNPC ta yi alkawarin baiwa ‘yan kasuwa man fetur kai tsaye.

Danmalam ya ce taron wanda ya gudana a karkashin NNPC, an yi shi ne domin lalubo hanyoyin magance matsalar karancin man fetur da ake fama da ita a kasar nan.

Danmalam ya ce dalilin da ya sa Kuluwu ya ba da wannan umarni shi ne saboda su ƴankasuwa na sayen fetur da tsada sosai saboda ba sa samun sa daga Defo sai dai defo din masu zaman kansu.

Ya kuma jaddada aniyar kungiyar na ci gaba da jigilar man zuwa dukkan jihohin kasar nan domin kawo karshen karancin kayayyakin da ake fama da su.

Ya ce Okoronkwo ya yi amfani da wannan dama wajen gargadin ‘yan kungiyar da kada su bari ‘yan siyasa su yi amfani da su domin cimma muradun su na son kai.