Home Labarai Ƴan IPOB sun kashe shugabannin al’umma 8 a Imo – Kwamishinan ƴansanda

Ƴan IPOB sun kashe shugabannin al’umma 8 a Imo – Kwamishinan ƴansanda

0
Ƴan IPOB sun kashe shugabannin al’umma 8 a Imo – Kwamishinan ƴansanda

Rundunar ƴansanda a jihar Imo ta ce yan bindiga, da ake kyautata zaton yan IPOB ne, a daren Asabar sun hallaka shugabannin al’umma a garin Umucheke dake karamar hukumar Onuimo.

Kwamishinan ƴan sanda, Aboki Danjuma ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da ya jagoranci shugabannin tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru.

Mista Danjuma ya zargi haramtacciyar ƙungiyar IPOB da kai harin.

Ya ce ƴan sanda da haɗin gwiwa da sojoji da Civil Defence na bibiyar dazukan dake kowaye da Okigwe domin zakulo maharan.

“Ɓata garin da suka kai harin sun kai 6”

Kwamishinan ya kara da cewa maharan sun zo a babura uku, kuma al’umma sun gansu kuma suka gaza kai rahotansu ga jami’an tsaro.

Ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa ransu inda ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro zasu zakulo maharan.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa wadanda aka kashe din sun hada da shugaban Hyginus Ohazurike da sauran shugabannin kauye guda 7.