
Gamaiyar ƙungiyoyi masu zaman kansu, a ƙarƙashin Hadaɗɗiyar Inuwar Ƙungiyoyi masu zaman kansu na Jihohin Arewa sun rubuta buɗaɗɗiyar wasiƙa ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a kan halin ƙuncin da Nijeriya ta tsinci kan ta.
A wasiƙar da Shugabannin ƙungiyoyi masu zaman kansu na jihohi 19 na Arewa su ka rattabawa hannu a ranar 9 ga watan Disamba, ƙungiyoyin sun baiyana cewa cire tallafin man fetur ba zai yiwu ba, ba zai samu nasara ba sannan bai kamata ba a halin da a ke ciki yanzu a Nijeriya.
A cewar ƙungiyoyin, a halin da a ke ciki na rashin tsaro, tashin gwauron zabi na farashin kayaiyaki, tsadar rayuwa da rashin aikin yi, “tabbas wannan tunanin na cire tallafin man fetur ba zai yi nasara ba.”
“Mai girma shugaban ƙasa, muna ma su baiyana maka damuwar mu da ta talakawan Nijeriya a kan ƙudurin ka ma cire tallafi mai a 2022.
“Mun san da cewa harkar mai ce ke da kaso mafi yawa wajen bunƙasar tattalin arzikin ƙasar nan, amma kuma ba a ganin tagomashin hakan sosai saboda tallafin da a ka sanya a kan man da a ke shigowa da shi da ga ƙasashen waje.
“Amma kuma tallafin da a ke biya na man da a ke shigowa da shi daga ƙasashen waje na da matukar amfani wajen sanya man fetur ya yi arha da kuma sauƙaƙa rayuwa.
“To gaskiya, dole ne mu ka hankali cewa ƙudurin cire man fetur ɗin nan wani lamari ne da ya kamata a sake yin duba a kai, ka da a yi shi gaba-gaɗi,” in ji ƙungiyoyin.
Sun kuma yi kira ga Buhari da ya farka da ga barcin da ya ke yi ya yi maganin matsalolin ƙasar nan da su ka jefa talaka a cikin halin ni-ƴa-su.