
Sanatan Kano ta tsakiya a majalisar dattawa ta Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya magantu tun bayan jingine batun zuwansa jihar Kano a gobe talata sabida dalilai na tsaro.
uni dai aka gayyaci tsohon Gwamnan fadar Shugaban kasa, domin yin tata tattaunawa ta musamman da mataimakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo.
A lokacin da yake magana da manema labarai a gidansa a ramar litinin, Kwankwaso yace, ya jingine batun zuwan nasa gida Kano ne, sabida kiraye kiraye da aka yi ta yi a gareshi, daga muhimman mutane daga kano da Abuja, wanda tilas ta sanya ya amsa musu.
“Ina son jama’a su sani ja da baya ga rago ba tsaro bane, kawai na ji kiran mutane ne a ciki da wajen kano domin samun zaman lafiya”
“Kusan shekara uku ban shiga jihar Kano ba, rabona da kano tun da na je ta’aziyar babar Ganude, dan haka na jima ban je kano ba”
Yace, wasu ‘yan Siyasa a jihar Kano sun hada kai da ‘yan sanda da wasu mutane anan Abuja domin hanani shiga kano.
“Yau ‘yan sanda sun mamaye cikin birnin Kano domin hana dan Kano shiga garinsa, wanda yana da ‘yanci”
“Ina cike da mamakin yadda ake yin neman kama karya a jihar Kano, ta hanyar kawo sojoji, kamar ana yin yaki” A cewar Kwankwaso.
Da aka tambayi Kwankwaso ko ya jingine batun zuwansa Kano ne sabida tsaro,yace yafi karfin jin tsoron wani mahaluki.
“Babu wani mahaluki da nake tsoro. Ni da nayi Ministan tsaron Najeriya, dukkan sojoji suke kirana da Yallabai, nine za’a kira matsoraci” A cewarsa.
Yace nan ba da jimawa ba, zamu sake sanya wata ranar da zamu je Kano, wannan lokacin kuma, sai yafi kowanne, domin zamu yi shirin da bamu yi ba a baya.