Home Labarai Jakolo ya caccaki Sultan da dattawan Arewa kan batun Dasuki

Jakolo ya caccaki Sultan da dattawan Arewa kan batun Dasuki

0
Jakolo ya caccaki Sultan da dattawan Arewa kan batun Dasuki

Tsohon dogarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zamanin da yake Gwamnan jihar Gwangola da kuma lokacin da yake Shugaban kasar Soja, Almustapha Haruna Jakolo ya caccaki Smai Alfarma Sarkin Musulmi da kungiyar dattawan Arewa kan yadda suna kallo ake cin mutuncin Sambo Dasuki da kuma yadda ake kin yi masa adalci.

Jakolo ya kira dattawan Arewar Munafukai marasa amfani da basa iya amfanawa kansu komai sai munafurci da makida. Jakolo wanda shi ne tsohon Sarkin Gwandu da aka cire a shekarar 2005, wanda ya garzaya kotu kuma kotu har karo biyu ta umarci da a mayar da shi kan karagar Mulkinsa.

Tsohon Sarkin Gwandun ya caccaki dattawan Arewa ne a lokacin da yake tattaunawa da jaridar Sun ta ranar Lahadi. Jakolo na magana ne akan yadda karara ake nunawa Dasuki rashin adalci wanda acewarsa dattawan Arewa sun ji muguwar kunya kan shirun da suka yi.