Home Siyasa Jam’iyar ADP ta tabbatar da takarar gwamna ta Sha’aban Sharada a Kano

Jam’iyar ADP ta tabbatar da takarar gwamna ta Sha’aban Sharada a Kano

0
Jam’iyar ADP ta tabbatar da takarar gwamna ta Sha’aban Sharada a Kano

 

Jam’iyyar Action Democratic Party, ADP, ta tabbatar da Sha’aban Sharada a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023 mai zuwa.

Sharada, wanda ke wakiltar mazabar Ƙaramar Hukumar Birni a majalisar wakilai ta kasa, ya koma ADP ne bayan ya sha kaye a zaɓen fidda-gwani na gwamna na jam’iyyar APC a ranar 27 ga watan Mayu.

Sakataren kungiyar ADP na jihar, Tasiu Abdurrahman ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Laraba a Kano cewa tabbatar da Sharada ɗin ya biyo bayan janyewar da dan takarar jam’iyyar, Nasiru Hassan Koguna ya yi don raɗin kansa.

“Kamar yadda kundin tsarin mulkin ADP ya tanada a irin wannan yanayi, ya kamata jami’an zartaswa su kafa kwamitin zaɓe da zai cike giɓin, wanda kuma ni ne shugaba.

“Mun gayyaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin ta shaida zaben sabon dan takara a ranar 12 ga watan Agusta, wanda shi ne wa’adin da hukumar ta tsayar na jam’iyyun siyasa su kammala sauya ‘yan takararsu na gwamna,” inji shi.

Abdurrahman ya ce dukkan mambobin kwamitin zartarwa na jam’iyyar 19 sun tabbatar da Sharada a matsayin sabon dan takarar gwamna.

Ya ce takarar ta Sharada ta ƙara wa jam’iyyar ADP damar lashe zaɓen gwamna a 2023 a jihar.

Sakataren shirya taron ya yi kira ga masu kishin jam’iyyar da su ci gaba da haɗa kan su tare da yin aiki tuƙuru domin samun nasarar jam’iyyar a zaben 2023.