Home Siyasa Jam’iyar APC ta tabbatar da dakatar da tsohon ɗan majalisar wakilai, Kumaila

Jam’iyar APC ta tabbatar da dakatar da tsohon ɗan majalisar wakilai, Kumaila

0
Jam’iyar APC ta tabbatar da dakatar da tsohon ɗan majalisar wakilai, Kumaila

 

 

 

Jam’iyyar APC a Jihar Borno ta tabbatar da dakatar da tsohon dan majalisar wakilai kuma shugaban marasa rinjaye, Mohammed Kumalia.

An dakatar da Kumalia, wanda ya wakilci mazabar birnin Maiduguri har sau biyu ne a ranar Litinin daga gundumarsa ta Limanti bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa.

Wata wasika da jam’iyar ta aike wa Kumalia, mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran jam’iyar na jihar, Makinta Zarami, ta ce kwamitin zartaswa na jam’iyyar na jihar ne ya amince da dakatarwar.

Ta ce ikirarin da Kumalia ya yi na cewa ya riga ya aike da takardar murabus kafin a dakatar da shi ihu ne bayan hari.

“jamiya ko a matakin mazaɓa, karamar hukuma ko jiha, ba ta samu wasikar ka ta murabus mai kwanan wata 21 ga Maris, 2022 ba.

” wannan ihu ne bayan hari don ka rufe gazawarka.

“Jam’iyyar ta ci gaba da cewa an dakatar da kai ne bayan duk zarge-zargen da ke kunshe a cikin wasikar dakatarwar daga gundumar Limanti,” in ji Zarami.

Wasu daga cikin zarge-zargen da ake yi wa Kumalia sun hada da gurfanar da jam’iyyar a gaban kotu wanda ya saba da sashi na 21 (2)(xi) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC na 2022 da aka yi wa kwaskwarima.

Sauran sun hada da rikon sakainar kashi a cikin ayyukan da suka saba wa sashi na 21(2) da kuma rashin da’a wanda ya sabawa sashi na 21 (2) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.