Home Siyasa Jam’iyyu 13 sun yi barazanar ficewa daga zaben 2023 idan CBN ta sake tsawaita wa’adin sauyin kuɗi

Jam’iyyu 13 sun yi barazanar ficewa daga zaben 2023 idan CBN ta sake tsawaita wa’adin sauyin kuɗi

0
Jam’iyyu 13 sun yi barazanar ficewa daga zaben 2023 idan CBN ta sake tsawaita wa’adin sauyin kuɗi

Kimanin jam’iyyun siyasa 13 da a ka yi wa rajista a Nijeriya sun yi barazanar ficewa daga zabukan da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga Maris idan har Babban Bankin Najeriya, CBN ya tsawaita wa’adinsa na musanya tsofaffin kudade da sababbi.

A tuna cewa babban bankin ya sanya ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin wa’adin musanyen, biyo bayan tsawaita wa’adin ranar 31 ga watan Janairu da ya yi.

DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa duk da tsawaita wa’adin, samun sabbin takardun ya zama wahala ga ƴan Nijeriya da dama.

Sai dai gwamnan na CBN ya dage cewa ba za a sake kara wa’adin ba.

Sai dai a lokacin da su ke magana da manema labarai a jiya Litinin a Abuja, gamayyar shugabannin jam’iyyun siyasan sun yi gargadin cewa ba za su shiga zabe ba idan har aka tsawaita wa’adin daga ranar 10 ga watan Fabrairu, kamar yadda wasu gwamnoni da jiga-jigan jam’iyyar APC suka bukata.

Da ya ke magana a madadin jam’iyyun, shugaban kungiyar Action Alliance, AA na kasa, Kenneth Udeze, ya caccaki gwamnatocin jihohin Kaduna, Kogi, da Zamfara kan yadda su ka garzaya kotun koli domin samun umarnin kotu na tsawaita wa’adin tabbatar da cigaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi guda uku.

Mista Udeze ya ce: “Muna sanar da cewa akalla jam’iyyun siyasa 13 daga cikin 18 na Najeriya ba za su yi shiga zaben 2023 ba, kuma lallai za mu janye daga shiga zaben muddin aka dakatar ko kuma soke wadannan manufofin kudin ko kuma idan an sake dage wa’adin.