Home Labarai JAMB ta saki sakamakon dalibai 1,502,978; ta rike na 112,331

JAMB ta saki sakamakon dalibai 1,502,978; ta rike na 112,331

0
JAMB ta saki sakamakon dalibai 1,502,978; ta rike na 112,331

Daga Hassan Y.A. Malik

Hukumar shirya jarrabawar share fagen shuga jami’a, JAMB ta saki sakamakon jarrabawar dalibai 1,502,978 (miliyan daya da dubu dari biyar da biyu da dari tara da saba’in da takwas) da suka zauna jarrabawar ta shekarar 2018.

A wata sanarwa da kakakin hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya fitar a jiya Talata a Abuja, ta ce, hukumar ta saki sakamakon jarrabawar ne bayan da ta kalli dukkan bidiyon da na’urar tsaro mai daukar bidiyo na dukkanin cibiyoyin da aka zana jarrabawar a fadin kasar nan tare da kuma yin nazarin rahotannin wakilan da hukumar ta tura don sanya idanu akan yadda jarrabawar ta gudana a dukkan cibiyoyi.

Hukumar ya bayyana cewa dalibai 1,652,825 ne suka zauna jarrabawar ta bana, amma hukumar bata saki sakamakon dalibai 112,331 (dubu dari daya da goma sha biyu da dari uku da talatin da daya).

Daga wannan adadi da ba a saki ba, a kwai sakamakon dalibai makafi 350 da hukumar za ta saki nan ba da jimawa ba, inda rragowar 111,981 (dubu dari da goma sha daya da dari tara da tamanin daya) za su fuskanci tantancewa mai tsanani kafin a saki sakamakon nasu.

Hukumar ta ce wannan sakamako bai shafi daliban da ba ‘yan asalin Nijeriya ba, wadanda za su rubuta jarrabawarsu a watan Afrilu mai zuwa.

Hukumar ta dada jaddada kudirinta na cewa ba za ta ci gaba da sakin sakamako nan da nan ba kamar yadda ta yi a shekarar jarrabawa ta bara, inda bayan da saki jarrabawar a ka samu kura-kurai nan da can.