Home Labarai Jami’ar Abuja ta kori Farfesoshi 2

Jami’ar Abuja ta kori Farfesoshi 2

0
Jami’ar Abuja ta kori Farfesoshi 2

 

 

 

 

Jami’ar Abuja ta bayyana ce wa ta kori wasu malamanta biyu, masu matsayin Farfesa, kan zargin neman ɗalibai mata domin su basu maki a jarrabawa.

Shugaban jami’ar, Farfesa Abdul-Rashaeed Na-Allah da ya ke bayyana labarin korar, ya ce jami’ar tana daukar tsau-tsauran mata kai akan malaman nata dake neman dalibai mata, inda ya kara da cewa hakan ne ya sanya ta kori malaman biyu akan irrin wananan laifin na amfani da dalibai mata kafin a basu maki su ci jarrabawa.

Na’Allah ya shaidawa kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN cewa jami’ar tuni ta kaddamar da dokoki da suka hana neman dalibai a cikin jami’ar baki daya.
Shugaban jami’ar wanda yanzu haka yana kasar Amerika domin haduwa da tsofafin daliban jam’ar, ya ce dalibai mata suna da bukatar a basu kariya ta kowa ce fuska.

Ya kara dacewa: “ abin takai ci ne kaga malaman da sune yakamata ace suna bawa daliban kariya da ga dukkan matsaloli kuma yanzu sune su ka zamo matsalar ta su.

“ duk da cewa wannan matsalar ta shafi jami’o’in najeriya ba wai iya jami’ar mu ce kadai ke fuskantar matsalar ba.
“yanzu haka akwai kwamatin da jami’ar ta kafa don yin binkice akan matsalar domin magan ce ta, yin hakan na daya daga cikin matsalolin da jami’ar zata magan ce ta shiga sahun zakakoran jami’o’in najeriya.

inda ya ƙara da cewa jami’ar tana kokari wajan habbaka kayan aiki ga dalibai, wadan da suka hada da na’urori na zamani a cikin jami’ar baki daya.