
Hukumar gudanarwar jami’ar Khalifa Isyaku Rabi’u, KHAIRU, ta kaddamar da kwamitin gudanarwa mai mutum 10 da za ta fara gudanar da ayyukanta.
Wanda ya kafa jami’ar, Nafiu Rabiu, yayin ƙaddamar da kwamitin a jiya Talata a Kano, ya dora ƴan kwamitin alhakin tabbatar da cewa jami’ar ta samu matsayin daraja ta farko a jami’o’i.
Malam Rabiu Isiyaku, wanda ya samu wakilcin mamba a hukumar, ya ce kafa jami’ar ya samo asali ne daga falsafa da da kuma soyayya ga ilimi da mahaifinsa, Marigayi Sheikh Khalifa Isyaku Rabi’u ke da ita.
Ya ce jajircewar marigayi Khalifa na kafa cibiyar a lokacin rayuwarsa ya baiwa ‘ya’yansa kwarin guiwar cika burin na sa.
Rabiu, ya ce da farko an sanya wa jami’ar sunan Jami’ar Attanzeel wanda ke nuna tsawon rayuwar Khalifa da sadaukar wa ga Alkur’ani mai girma.
Ya bayyana cewa Hukumar kula da Jami’o’i ta Ƙasa, NUC, ce ta bada umarnin canja wa jami’ar suna zuwa Jami’ar Khalifa Isyaku Rabi’u.