Home Labarai Jami’ar Madina ta karrama Farfesa Alaro na jami’ar Ilorin

Jami’ar Madina ta karrama Farfesa Alaro na jami’ar Ilorin

0
Jami’ar Madina ta karrama Farfesa Alaro na jami’ar Ilorin

 

Jami’ar Musulunci ta Madina da ke Ƙasar Saudiyya, ta karrama Farfesa AbdulRazzaq Alaro, Shugaban Sashen Shari’ar Musulunci na Jami’ar Ilorin, a matsayin ɗaya daga cikin gwarazan tsofaffin ɗalibanta guda 10.

Alaro ya samu digirinsa na farko, Diploma a fannin ilimi da kuma digiri na biyu da kuma digirin digirgir daga jami’ar da ke Saudiyya a 1993, 1997 da 2002, bi da bi.

Jami’ar Ilorin ta bayyana hakan ne a cikin mujallarta a yau Litinin, inda ta ce jami’ar ta Saudiyya ta ba da wannan karramawa ne domin yabawa irin gudunmawar da Alaro ya bayar wajen yaɗa addinin Musulunci da kuma ci gaban ilimi.

Ya ƙara da cewa Jami’ar Madina musamman ta fahimci irin nasarorin da Alaro ya samu wajen koyar da fannin shari’ar Musulunci tun bayan kammala karatunsa na digiri na farko a jami’ar kimanin shekaru 30 da su ka gabata.

“Shahararren malamin yana cikin ƴan tsirarun ƴan Afirka da ƴan Nijeriya da aka karrama, wanda ya gudana a jami’ar ta Saudiyya a farkon watan Yuni.

“Alaro shi ne kuma shugaban kwamitin bincike da fassara na kungiyar malaman Afirka da ke Bamako,” in ji shi.

Mujallar ta Jami’ar Ilorin ta bayyana cewa, da ya ke tsokaci a kan karramawar, Farfesa Alaro ya bayyana matuƙar godiyarsa ga Allah da Ya sa ya cancanci karramawa idan aka yi la’akari da dimbin tsofaffin daliban jami’ar.

“Ya yi nuni da cewa kyautar za ta ƙara masa kwarin gwiwar yin aiki tukuru, ya kuma yi alkawarin ci gaba da zama jakadan nagari a jami’ar Saudiyya,”