
Wata cibiyar bincike mai suna SCImago da ga jami’ar Granada a ƙasar Spain ta bayyana jami’ar tarayya ta Dutse, FUD a matsayin jami’a ta farko a nahiyar Afrika da ta yi fice a ɓangaren lissafi, wanda a ka fi sani da mathematics, a cikin jami’o’i 422 da aka tantance a duniya.
Idan za a tuna cewa matasa uku masu a bangaren koyarwa a FUD; Dr.Tukur Abdulqadir Suleiman,Dr.Aliyu Isa Aliyu da Dr. Abdullahi Yusuf, dukkan su a sashin koyar da lissafi a jami’ar, su ka shiga jerin kashi 2 cikin ɗari da su ka yi fice a fannin kimiya da a ka fi buga misali da sakamakon binciken a duniya da wata cibiyar bincike, ƙarƙashin jagorancin Farfesa John Loannidis na Jami’ar Stanford, California, a Amurka ta fitar.
A rahoton jerin matsayi na 2022 da SCImago ta fitar a kwanan nan, FUD na matsayi na 43 a fannin kirkire-kirkire a Afirka da kuma ta 55 a fannin bincike a Afirka sai kuma ta zama ta 66 gabaɗaya a Afirka daga cikin Jami’o’in 422.
Hakazalika a jadawalin matsayi a jami’o’in Nijeriya da SCImago ta fitar, FUD ce jami’a ta 10 a gaba ɗaya a Nijeriya, yayin da jami’ar kuma ta zama ta 13 a fannin bincike da kuma na 9 a fannin kirkire-kirkire a Nijeriya.
Cibiyar SCImago na aiki ne wajen tantance cibiyoyi mna fannin karatun jami’a da bincike, inda ta ke fitar da jami’o’i da cibiyoyi da su ka yi fice a harkar koyarwa jami’a da kuma bincike.
Shugaban jami’ar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ya taya ma’aikata da daliban jami’ar murnar wannan gagarumar nasara da aka samu, inda ya ƙara da cewa nasarorin da aka samu a ƙarƙashin sa a cikin shekara ɗaya da ta wuce ya dogara ne da jajircewa da sadaukarwar ma’aikatan da daliban jami’ar.
Ya kuma kara da cewa in dai jami’ar na son dorewa da irin wannan nasarori, to dole sai kowa ya bada gudunmawa.