
Hadimin tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan, Mista Reno Omokri yaa bayyana sunayen baraayin Najeriya da suka daka wawa a cikin dukiyar Gwamnati wanda suke cikin Gwamnatin Buhari da jam’iyyar APC mai mulkin.
Ga sunayen mutanan da ya zayyana da kuma adadin kudaden da suka sata:
Rotimi Amaechi: An same shi da laifi wawure kudin Naira biliyan 97 karkashin kwamitin bincike da aka kafa masa wanda Mai Shari’ah George Omeregi ya jagoranta a jihar Ribas.
Ibrahim Saminu Turaki: Tsohon Gwamnan jigawa ne, ya saci kudin gwamnatin jihar Kimanin Naira biliyan 36. Har an gurfanar da shi a gaban kotu inda mai shari’ah Sabi’u Yahuza na babbar kotun Shariah dake Dutse a jihar Jigawa, inda aka mayar da Shairar tasa babban birnin tarayya gaban mai Shari’ah Namdi Dimgba.
Timipre Sylva: Tsohon Gwamnan jihar Bayelsa, wanda kuma fitacce ne wajen taimakawa Gwamnatin Buhari da kudaden kamfen. An same shi da laifi kwashe zunzurutun kudi Naira biliyan 19.7. Yanzu haka yana fuskantar Shari’ah gaban mai shariah A.Y. Mohammed a babbar kotun tarayya dake Abuja.
Haka kuma, kwanaki biyu bayan rantsar da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Gwamnatin tarayya karkashin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanya aka kori shari’ar da ake yiwa Sylva a ranar 1 ga watan Yunin 2015, haka kuma, a ranar 3 ga watan Oktoba na shekarar 2018 hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta mayarwa da Sylva da gidaje 48 wanda ta kwace daga hannunsa a zamanin Gwamnatin Jonathan a shekarar 2013.
Sauran barayin sune:
Murtala Nyako: Ya kashe zambar kudi naira biliyan 29. Yanzu haka yana fuskantar Shariah gaban Alkalin babbar kotun tarayya Okon Abang dake maitama a babban birnitarayya dake Abuja.
Sanata Danjuma Goje: Ya sace Naira biliyan 25 a lokacin da yake Gwamnan jihar Gombe. Yanzu haka yana fuskantar Shari’ah a gaban babbar kotun tarayya dake zamanta a Jos babban birnin jihar Filatu.
Sanata Abdullahi Adamu: Ya sace naira biliyan 15 tare da taimakon wasu mutane 18 da ake yi musu Shari’ah tare. An kuma gurfanar da su a ranar 3 ga watan maris na shekarar 2010, har yanzu ana kan yi masa Shari’ah a kotu.
Orji Kalu: Ya sace naira biliyan 3.2. Yanzu haka yana fuskantar Shari’ah a gaban babbar kotun tarayya dake zamanta a Legas gaban mai Shari’ah Mohammed Idris.
Kayode Fayemi: Kwamitin bincike da Babban jojin jihar Ekiti ya jagoranta tare da Babban basaraken jihar Oluyin na Iyin-Ekiti, Ademola Ajakaiye sun sami Fayemi da zambar kudade da ta kai Naira biliyan 2.
Sanata Joshua Dariye: Ya saci Naira biliyan 1.2. Yanzu haka yana fuskantar Shari’ah a babbar kotun tarayya dake Abuja gaban Mai Shari’ah Adebukola Banjoko.
Babachir Lawal: Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari. Ya baiwa kansa kwangilar Naira miliyan 200 kudin da aka ware domin ‘yan gudun hijira dake yankin Arewa maso gabas. Ancire shi daga mukaminsa bayan da ‘yan adawa suka yi ta yamadidi da batun, har yanzu haka yana gaban kotu ana tuhumarsa. Aka kuma bashi damar ya kawo dan uwansa domin ya gaji mukaminsa.
Duba da wadannan sunaye, Gwamnatin Buhari cike take da miyagun barayin da suka talauta jihohinsu dama Najeriya baki daya.