Home Kanun Labarai Jami’an Tsaro sun kama Sanata Dino Melaye

Jami’an Tsaro sun kama Sanata Dino Melaye

0
Jami’an Tsaro sun kama Sanata Dino Melaye

Daga Hassan Y.A. Malik

Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta Kudu a majalisar dattijai na kasar Nijeriya, Dino Melaye, ya ce jami’an tsaro sun cafke shi a filin jirgin saman Abuja.

Sanatan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a safiyar Litinin, inda ya ruwaito kamar haka:

“I have just been arrested at the international wing of the Nnamdi Azikiwe airport on my way to Morocco for an official engagement sponsored by the Federal Govt after checking in.”

Ma’ana: “An cafke ni a bangaren da fasinjojin masu fita kasan waje ke zama na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwa a yayin da na ke shirin zuwa Morocco a wata tafiya ta musamman wanda gwamnatin kasa ta biya min.”