
Daga Hassan Y.A. Malik
Jam’iyyar adawa ta PDP ta zargi jam’iyya mai mulki ta APC da shigo da makamai Nijeriya, wadanda ake amfani da su wajen aikata kashe-kashe a fadin kasar nan.
Jam’iyyar ta bukaci shugaban kasa Buhari da rundunar sojin kasa da su fito fili su fada wa ‘yan Nijeriya yadda makamai ke shigowa Nijeriya daga kasashen waje kuma suka shiga hannun bata gari iri iri.
Jam’iyyar na kuma zargin gwamnan jahar Kogi da mambobin APC reshen jahar da kasancewa da hannu a cikin shigo da makaman.
A don haka ne ma su ke bukata a bincike gwamnan da makarraban sa.
PDP ta kuma zargi APC da yi wa zaman lafiyar kasar barazana da niyyar tsoratar da masu zabe a shekara mai zuwa ta 2019.
Wadannan batutuwa dai na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar a yau Asabar, inda ya ce sun samu rahotanni game da yadda makamai ke shiga hannun wadanda ke kashe-kashe a kasar.
Ya ce kuma wadannan rahotanni sun nuna masu cewa wasu daga cikin mambobin APC ne ke taka rawa wajen satar shigo da makaman.
PDP ta ce ta na bukatar a gudanar da bincike a bayyane domin ‘yan Nijeriya sun san gaskiyar wannan lamari.